Mali

Rashin tabbas bayan juyin mulki a kasar Mali

Shugaban gwamnatin mulkin soja ta Mali Amadou Sanogo
Shugaban gwamnatin mulkin soja ta Mali Amadou Sanogo Habibou Kouyate / AFP

Shugaban sabuwar gwamnatin mulkin sojan kasar Mali Capt Amadou Sanogo ya bayyana cewa ba za a muzanta tsaffin jami’an gwamnatin kasar.Ya bayyana shirin gudanar da zabe da zaran lamura sun daidaita cikin kasar mai fuskantar tawaye daga Azbinawa a yankin arewaci.

Talla

Kungiyar Tarayyar Afrika ta dakatar da kasar ta Mali. Yayin da ake ci gaba da tararrabi inda hambararren Shugaba Amadou Toumani Toure yake yanzu haka. Dukda yake kungiyar ta ce ambata tabbatacin cewa Toure yana cikin koshin lafiya bayan juyin mulkin, kuma yana kusa da Bamako babban birnin kasar ta Mali.

Yawancin kungiyoyin duniya da masu bada agaji sun dakatar da kasar bayan juyin mulkin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI