Isa ga babban shafi
Senegal

Kasashen Duniya sun yaba da zaben kasar Senegal da Dan adawa Sall ya lashe

REUTERS/Finbarr O'Reilly
Zubin rubutu: Suleiman Babayo | Garba Aliyu
Minti 1

Shugabannin kasashen duniya dana kasashen Afrika nata aikewa kasar Senegal sakonnin tayasu murna saboda yadda aka gudanar da zaben kasar zagaye na biyu cikin kwanciyar hankali, har aka kawar da Shugaba maici Abdoullaye Wade ba tare da rudani ba.

Talla

Jakadiyar kasashen Turai Uwargida Cathrine Ashton, ta bakin kakakin ta Micheal Mann ta ce mutanen kasar Senegal sun ci a yaba masu,

Wani wakili a MDD Said Djinmit ya ce majalisar ta yabawa da yadda mutanen kasar Senegal suka bi komi cikin tsanaki.

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy, kasar data reni Senegal, anashi sakon ya ce sakamakon zaben ya faranta zuciyar mutanen nahiyar Africa da duniya baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.