Isa ga babban shafi
ECOWAS-CEDEAO

Shugabannin kasashen Afrika ta Yamma na taro kan juyin mulkin kasar Mali

Zubin rubutu: Garba Aliyu | Suleiman Babayo
Minti 1

Shugabannin kasashen Yammacin Africa na wani taro na musamman yau Talata, a birnin Abidjan kasar Cote d'Ivoire, game da halin juyin mulki da aka samu a kasar Mali, kasa da mako daya da sojan kasar ta Mali karkashin Capt Amadou Sanogo, suka yi kukar kura suka kifar da Gwamnatin farar hulan kasar ta Amadou Toumani Toure.

Talla

Shugabannin kasashe takwas daga cikin kasashe 15 ke halartan taron na gaggawa.

Shugaban kasar ta Cote d’Ivoire Alassane Ouattara, wanda ya ke rike da ragamar Shugabancin kungiyar ke shugabancin taron na yau.

Akwai yuwuwar dakatar da kasar ta Mali, daga cikin kungiyar kamar yadda aka yiwa sauran kasashen da sojoji suka kifar da gwamnati. Kuma ana iya saka takunkumi karya tattalin arziki wa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.