ECOWAS-Mali

ECOWAS ta dakatar da Mali saboda juyin mulki

Shugaban kungiyar ECOWAS Alassane Ouattara a lokacin da yake jagorantar taron gaggawa game da kasar Mali.
Shugaban kungiyar ECOWAS Alassane Ouattara a lokacin da yake jagorantar taron gaggawa game da kasar Mali. REUTERS/Thierry Gouegnon

Kungiyar kasashen Yammacin Afrika ECOWAS ta dakatar da wakilcin kasar Mali a kungiyar saboda juyin mulkin da Sojoji suka yi na hambarar da gwamnatin Farar hula ta Amadou Toumani Toure. Kungiyar ta cim ma matakin tura wasu Wakilanta Zuwa Mali domin tattauna yadda za’a dawo da kasar tafarkin demokradiyya.

Talla

Sai dai kuma a kafar Telebijin, gwamnatin Sojin Mali ta bayyana sabon Kundin tsarin mulkin kasar wanda ya kunshi ‘Yancin Fadin albarkacin baki da zirga-zirga.

Kuma bubu wani tabbaci da Gwamnatin Soji ta bayar game da mayar da gwamnatin da aka hamabarar ta Farar hula, kamar yadda masu makwabtaka da kasar suka bukata.

Sojojin kasar sun hambarar da gwamnatin Amadou Toumani Toure ne saboda rashin gamsuwa da tsarin shi na magance rikicin ‘Yan tawayen Azbinawa a Arewacin Mali.

Matakin dakatar da Mali daga ECOWAS ya biyo bayan wani taron gaggauwa ne da shugabannin kungiyar suka gudanar a birnin Abidjan na kasar Cote d’Ivoire.

Ana sa ran shugaban kungiyar, Alassane Ouattara shi zai jagoranci tawagar ECOWAS zuwa Mali tare da shugaban kasar Benin da Burkina Faso da Nijar da Liberia.

Tun a jiya Talata ne Sabuwar gwamnatin Sojin kasar Mali ta bukaci ma’aikata komawa aikinsu tare da janye dokar hana fita da ta fara bayan karbe ikon kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI