Isa ga babban shafi
Mali

Hambararren Shugaban Mali Toure ya shaidawa gidan rediyon Faransa yana cikin Mali

Hambararren Shugaban Mali Amadou Toumani Touré
Hambararren Shugaban Mali Amadou Toumani Touré Getty Images
Zubin rubutu: Suleiman Babayo
Minti 1

Hambararren Shugaban kasar Mali Amadou oumani Toure, da sojoji suka kifar da gwamnatinsa ranar Laraba 21 ga watan na Maris, ya bayyana cewa baya hanun sojojin da suka yi juyin mulki.Toure ya ce yana Bamako babban birnin kasar, kamar yadda ya tabbatarwa gidan rediyon Faransa, RFI, cikin gajeruwar hira ta waya. 

Talla

Makomar hambararren Shugaba Toure, dan shekaru 63 da haihuwa, ya zama abun damuwa kwanaki shida bayan sojoji karkashin Capt Amadou Sanogo sun kifar da gwamnatin kasar ta Mali.

Jakadan Faransa Christian Rouyer, dake kasar ta Mali, yana cikin wadanda suka tuntubi hambararren Shugaba Toumani Toure ta waya.

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS-CEDEAO, ta dakatar da kasar ta Mali, tare da tura wakilai, domin ganawa, ta hanayar mayar da kasar bisa tafarkin demokaradiya. Sojoji sun ce babu dayansu da zai tsaya takaran zaben da zasu gudanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.