MDD

MDD ta nuna damuwa kan fada tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya, da Kungiyar kasahsen Afrika sun bayyana damuwarsu kan fadan da ya barke a iyakokin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu, inda Sudan ta ci gaba da kai hare hare kan yankunan Suda ta kudu.Ganin yadda ake ci gaba da kai hare haren sama da kasa a Yankin kan iyakokin kasashen biyu, Majalisar Dinkin Duniya ta bayayna damuwar ta, inda ta bukaci kasahsen biyu, su yi taka tsantsan, da kuma komawa teburin sasantawa. 

Talla

Ita ma kungiyar kasashen Afrika ta AU, ta hannun shugaban gudanarwar ta, Jean Ping, ta ce babu yadda za’a magance rashin fahimtar juna ta fada, dole sai an koma teburin shawara, inda ta bukaci Gwamnatocin biyu su janye dakarun su kilomita goma daga kan iyakokin kasahsen.

Rahotanni sun ce, an kwashe kwanaki biyu ana fafatwa tsakanin kasashen biyu, yayin da Ministan yada labaran Jihar Unity, Gideon Gatpan, ya tabbatar da janyewar sojin kasa, amma kuma ya ce Sudan ta ci gaba da ruwan wuta ta jiragen sama.

Wakilin kanfanin Dillancin labaran Faransa a Sudan, wanda ya isa garin Heglig tare da Ministan man kasar, Awad Ahmad al Jaz, tare da Gwamnan South Kordafan, Ahmed Harun, ya ce ya ga gawauwaki da dama, yayin da hayaki ya turnike Yankin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.