Gwamnatin mulkin sojan Mali ta nemi taimakon yakan 'yan tawayen Azbinawa
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Mali, Capt Amadou Sanogo, ya nemi tallafin kasashen duniya, domin kawar da ‘yan tawayen Azbinawa na Arewaci dake ci gaba da dannawa inda suka kama garin Kidal mai mahimmanci.Kirar shugaban ya zo kwana guda, bayan kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS-CEDEAO ta bada wa’adin kwanaki, na mayar da mulki kasar ga zababbiyar gwamnatin farar hula da aka hambarar.
Yayin taron manema labarai sabon shugaban Sanogo, ya nemi kawayan kasar ta Mali, su kawo dauki, domin tabbatar da iyocin kasar.
Tun cikin watan Janairu Azbiwa kasar suka zari makamai suna yakan gwamnati, domin samar da ‘yan wa yankin Azbinawa.
Juyin juya halin kasar Libya, da ya kai ga kifar da gwamnatin Magayi Shugaba Muammar Gaddafi, ya janyo yaduwar makamai cikin kasashen Afrika ta Yamma, abunda ke haddasa tashe tashen hankula a wannan yanki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu