Sharhin Jaridu

Sharhin wasu Jaridun Afrika

Jaridu a Taswirar Africa
Jaridu a Taswirar Africa

Jaridu a kasar Kenya sun ruwaito labarin kashe Rail Odinga, ko su wane ne? ko Ministan kudin Najeriya Ngozi zata taimaka wajen yaki da karancin abinci mai gina jiki a kananan yara a duniya? Yaya Joyce Banda zata daidaita al’amurra a kasar Malawi? Ko me yasa babu ‘Yan Afrika da yawa a gasar ‘Yan Luwadi ta duniya?

Talla

Jaridar Daily Nation a kasar Kenya ta ruwaito labari mai daga hankali daga kabilar Kisumu da ake zargin suna yunkurin kisan Fira Ministan kasar Rail Odinga.

A cewar Jaridar, akwai rashin jituwa da aka samu tsakanin kabilar Lua da Kisii. Kuma wani dan Majalisa ne Jakoyo Midiwo ya gabatar da zargin. Sai dai Jaridar tace Mzalendo N Kibunjia shugaban hukumar sasantawa yace ‘Yan Sanda zasu gudanar da bincike game da lamarin.

A Najeriya, Jaridar Punch ta ruwaito wani mukami da aka ba Ngozi Okonjo-Iwaela domin taimakawa wajen warware matsalar karancin abinci mai gina jiki ga kananan yara a duniya.

Wannan kuma na zuwa ne bayan Ministar ta amsa tambayoyi domin shugabantar Babban Bankin Duniya.

Yawancin Jaridun Najeriya suna goyon bayan takarar Ngozi domin samun mukamin Bankin Duniya.

Jaridar Guardian a kasar Afrika ta Kudu ta ruwaito labari game da yunkurin Joyce Banda wajen kokarin kawo sauyi a kasar Malawi bayan mutuwar Bingu Wa Mutharika.

Sai dai bayan rantsar da Banda, ta sallami wasu manyan na hannun damar marigayi Wa Mutharika.

A kasar Kenya, Jaridar Daily Nation ta ruwaito labari game da yadda ‘Yan kasashen Afrika suka fice daga gasar kyau ta ‘Yan Luwadi ta duniya.

Jaridar tace ‘Yan takara da suka shiga gasar daga kasar Habasha da Zimbabwe da Tanzania sun fice gasar tare da wasu ‘yan kasar Kenya guda uku saboda matsin lamba daga gwamnatocin kasashensu da kuma rashin tallafi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.