Najeriya-Birtaniya

Kotun Birtaniya ta yankewa Ibori Hukuncin dauri shekaru 13

James Ibori Tsohon Gwamnan Jahar Delta a Najeriya
James Ibori Tsohon Gwamnan Jahar Delta a Najeriya

Kotun Birtaniya ta yanke hukuncin daurin shekaru 13 ga James Ibori tsohon gwamnan Jahar Delta a Najeriya bayan kama shi da lafin sace kudaden al’ummar Jahar shi Dala Miliyan 250.

Talla

James Ibori mai shekaru 49 na haihuwa shi ne Gwamnan Jahar Delta tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, a jiya Talata ne Kotun Southwark Crown a London ta yanke masa hukunci.

Zaman kotun na farko a ranar Talata an tashi ba shiri, lokacin da wasu magoya bayan Ibori suka mamaye kotun. Ana zargin cewa Gwamnatin Jihar Delta ce ta dauki nauyin su.

‘Yan Sandan London sai da suka yi amfani da jirgin sama mai saukar ungulu, da motoci takwas, wajen kai jami’an tsaro domin kaucewa tashin hankali a zaman kotun.

Mista Ibori ya fuskanci shari’a ne a Birtaniya bayan zargin shi da sace kudaden Gwamnati.

Ibori yana karbar albashin kudi Dala 25,000 a wata a lokacin da yana Gwamna amma an zarge shi da mallakar Gida a Birnin London da ya yi tsadar kudi Fam Miliyan 2.2 tare da mallakar wani gidan da ya yi tsadar kudi Fam Miliyan 3.2 a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta kudu.

An bayyana Ibori ya mallaki Jirgin sama da ya yi tsadar kudi Dala Miliyan 20 tare da mallakar wasu manyan motoci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.