Najeriya

Majalisar Wakilan Najeriya ta yi kiran hukunta barayin tallafin Mai

Wasu 'Yan Najeriya a lokacin Zanga Zangar adawa da Janye Tallafin Mai
Wasu 'Yan Najeriya a lokacin Zanga Zangar adawa da Janye Tallafin Mai Reuters

Kwamitin Lawan Faruk mai binciken badakalar bangaren Man fetir a Najeriya yace an sace kudade Dalar Amurka Biliyan Shida daga kudaden Tallafin Gwamnati a shekarun da suka gabata. Majalisar Wakilan Najeriya ta nuna bacin ranta kan yadda wasu jami’an Gwamnati da kamfanoni suke rub da ciki da dukiyar kasa da sunan tallafin man fetur.  

Talla

Majalisar ta amince da shawarwarin da kwamitin Faruk Lawal ya gabatar domin daukar mataki akansu.

An nada kwamitin binciken ne karkashin jagorancin Dan Majalisa Faruk Lawan daga Jahar Kano sanadiyar boren da aka kwashe tsawon mako ana gudanarwa saboda janye tallafin Mai a watan Janairu.

Najeriya tana cikin manyan kasashe masu samar da Mai a Duniya amma yawancin Man da Najeriya ke amfani da shi daga waje ake shigowa da shi.

Kakakin Majalisar Aminu Waziri Tambuwal yace zasu yi kokarin kwato wa Talakawa hakkinsu.

Rehoton Majalisar mai yawan shafi 205 ya zayyana hukumomin da suke da hannu a badakalar karkatar da Tallafin da suka hada da Kamfanin Mai na NNPC da wasu‘Yan kasuwa

A cewar Rehoton akwai ‘Yan kasuwa masu shigo da mai 15 da suka karbi kudade Dala Miliyan 300 shekaru biyu da suka gabata ba tare da sun shigo da Man a Najeriya ba.

Rehoton yace akwai ‘Yan kasuwa da dama da ke karbar makudan kudade ba tare biyan bukata ba.

Akwai wasu manyan Jami’an gwamnatin Goodluck Jonathan da rehoton ya bayyana suna cin gajiyar kudaden Tallafin.

Sai dai wadanda ake zarga da wawure kudade Jama’a sun musanta zargin.

A ranar 1 ga watan Janairu ne Shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana Janye Tallafin Mai da gwamnatin Najeriya ke bayarwa al’amarin da yasa Kungiyar kwadago da kungiyoyin farar hula suka tsunduma cikin yajin aiki saboda karin farashin man daga N65 zuwa N141.

An kwashe tsawon mako daya ana gudanar da zanga-zanga a sassan yankuna Najeriya kafin janye yajin aikin bayan gwamnati ta sasanta da Kungiyoyin kwadago inda ta mayar da Farashin Mai zuwa N97.

Duk da matsayin Najeriya cikin manyan kasashe masu samar da Mai a Duniya har yanzu babu wasu kudade da Najeriya ta kashe domin gyara matatun man kasar.

Al’ummar Najeriya da dama suna ganin Tallafin Mai shi ne hanya daya da suke more arzikin da Allah ya albarkaci kasar da shi.

Amma Goodluck Jonathan yace janye Tallafin Mai ita ce hanya mafita da za’a inganta tattalin arzikin Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.