Sharhin Jaridu

Sharhin Wasu Jaridun Afrika

Jaridun Afrika a cikin Taswirar Afrika
Jaridun Afrika a cikin Taswirar Afrika

Dakatar da aikin wasu Alkalan Kenya, da sauraren karar tsohon shugaban kasar Liberia Cherles Taylor a Hague da kuma jerin sunayen mutane Ashirin masu karfin fada aji a Nahiyar Afrika su ne labaran da suka mamaye yawancin Jaridun Afrika.

Talla

A jiya Laraba ne aka dakatar da aikin wasu Alkalan Kenya guda hudu bayan fahimtar rashin cancantarsu a aikin alkalanci.

Jaridar Standard tace dakatar da Alkalan, mataki ne na kokarin inganta bangaren shari’a a Kenya.

Cikin Alkalan da aka sallama sun hada da shugaban kotun kolin kasar wanda yana cikin manyan alkalai a Kenya.

A jiya Laraba ne kuma Mujallar Forbes ta fitar da jerin sunayen mutanen Afrika 20 da suka kunshi mata da maza masu karfin fada aji a Nahiyar. Kuma a cewar Jaridar Star ta kasar Afrika ta kudu tace 12 daga cikinsu ‘yan kasar Afrika ta Kudu ne.

Jaridar Inquirer a kasar Liberia ta yi sharhi game da sauraren karar tsohon shugaban kasar Charles Taylor wanda ake zargi da aikata laifukan yaki.

Jaridar ta ruwaito kalaman John Whitfield, tsohon babban Jami’in gwamnatin Charles Taylor yana cewa akwai tasirin siyasa a zargin da ake wa maigidansa. Mista John yace akwai bakin masu karfin fada a ji a shari’a Taylor don haka yana da wahala a wanke shi.

Sai dai Jaridar tace tsohon Ministan kwadagon kasar Tiawon Gongoloe, yace babu tantama sai an samu Taylor da laifi.

Ana zargin Taylor ne da aikata laifuka 11 da suka hada da laifukan yaki, da keta hakkin Bil’dama da wasu laifukan da suka keta dokar cin zarafin Dan Adam ta Duniya da ya bayar da umurni tsakanin 1996 zuwa 2002. Amma Taylor ya karyata dukkanin zarge-zagen da ake masa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.