Chad-Najeriya

Gwamnatin Chadi ta nemi samar da dakarun hadin kai don yaki da Boko Haram

Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya Iman Abubakar Shekau a sakonsa ga shugaba Jonathan.
Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya Iman Abubakar Shekau a sakonsa ga shugaba Jonathan. REUTERS/IntelCenter/Handout

Gwamnatin kasar Chadi ta yi kiran kasashen 16 a kungiyar raya tafkin Chadi domin samar da dakarun hadin kai don yaki da ‘Yan kungiyar Boko Haram da ke barazana ga sha'anin tsaro a Najeriya da makwabtanta.

Talla

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a taron kungiyar da ake yi a birnin Libreville na kasar Gabon.

A cewar Shugaban ya zama wajibi mambobin kasashe 16 masu ruwa da tsaki game da tafkin Chadi, su kafa Dakarun hadin gwiwa, ganin yadda ‘Yan kungiyar Boko Haram ke neman durkusar da Najeriya.

Mista Deby Yace illar ‘Yan kungiyar Boko Haram, tafi ta tafkin Chadi.

Deby ya samu goyon bayan Shugaban kasar Tsakiyar Africa Francois Bozize, wanda yace zai bada gudunmawar Dakarun kasarsa domin samar da Dakarun hadin kan.

Taron kungiyar kasashen yana da niyyar farfado da tafkin Chadi ne, wanda dimbin jama’a ke dogaro da shi don rayuwa.

Kungiyar Raya Tafkin Chadin ta kunshi Kamaru da Jamhuriyar Tsakiyar Africa da Chad da Libya da Nijar da Najeriya.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.