Zimbabwe-Sabon kundi

komitin da ke kula da tsara sabon kundin tsarin mulkin kasar Zmbabwe ya kusa kammala aikinsa

komitin majalisar dokoki dake kula da tsara sabon kundin tsarin mulkin kasar Zimbabwe, na dab da kammala aikin samar da sabon kundin tsarin mulki ga kasar.An bayyana cewa, aikin samada da kundin yanzu haka ya kai ga matakinsa na karshe, kamar yadda yarjejeniyar siyasar da aka cimma, wace ta biyo bayan tashe tashen hankullan da suka barke a lokacin zaben shekara ta 2008 ya tanada, kafin gudanar da wani sabon zabe a kasar.