Najeriya

An kwana ana musayar albarussai a Kano tsakanin Jami'an tsaro da 'Yan Boko Haram

Wasu motocin yakin Jami'an tsaro a Najeriya da aka gani a harabar Jami'ar Bayero a Kano bayan 'Yan bindiga sun kai hari inda suka kashe mutane 20
Wasu motocin yakin Jami'an tsaro a Najeriya da aka gani a harabar Jami'ar Bayero a Kano bayan 'Yan bindiga sun kai hari inda suka kashe mutane 20 REUTERS/Stringer

A birnin Kano a Najeriya an kwashe daren jiya ana musayar Al barussai tsakanin Jami’an tsaro da wasu da ake zargin ‘Yan kungiyar Boko Haram ne. Wakilin RFI yace Jami’an tsaro ne suka kai samame a yankin sharada zuwa unguwar Sabuwar Gandu a wani gida da suke zargin mafakar 'Yan Boko Haram.

Talla

Bayanan da muka samu na cewa tun daga misalin karfe 2:30 na dare har zuwa wayewar gari ake jin karar bindiga a birnin Kano.

Zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani da aka samu, ko an samu rasa rai da jikkata.

A karshen mako ne wasu ‘Yan bindiga suka kai hari a wajen ibadar mabiya addinin Kirista a Jami’ar Bayero a Kano inda aka samu mutuwar mutane 20.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.