Libya-Autriche

Mutuwar tsohon PM kasar Libiya Shukri Ghenem ba abin damuwa bace ga yan kasar…

Choukri Ghanem, en 2004 lors d'une visite à Tunis.
Choukri Ghanem, en 2004 lors d'une visite à Tunis. AFP PHOTO/FETHI BELAID

Har zuwa yau talata ba san dalilin mutuwar Shukri Ghenem tsohon PM, haka kuma ministan mai a kasar Libiya ba.A ranar assabar 28 ga watan jiya na Avrilu ne, aka samu gawar Shukuri Ghenem daya daga cikin na kusan tsohon shugaban kasar Libiya Ma’amar kaddafi a wani kududdufi dake Danube a birnin Vienne na kasar Autriche.Amma kuma rahotanni daga Libiya na nuna cewa, yan Libiya sun bayyana cewa basu damu ba dangane da mutuwar tsohon PM kasar, wanda dama yake cikin mutanen da mahukumtan na Libiya ke bukatar ganin ya fada hannunsu.Yanzu haka dai mahukumtan kasar Autriche na ci gaba da gudanar da bincike domin gano masabbabin mutuwar tasa.