Sudan-Sudan ta Kudu

Rasha ta nemi kar a sakawa kasashen Sudan takumkumi saboda yakin da suke yi

Serguei Lavrov et Ali Karti le 30 avril 2012 à Moscou.
Serguei Lavrov et Ali Karti le 30 avril 2012 à Moscou. REUTERS/Denis Sinyakov

Kasashen China da Russia sun tsaya kai da fata cewa atafau, kada MDD ta cigaba da barazanar kakabawa kasashen Sudan da Sudan ta kudu wani takunkumi saboda sunki tsagaita wuta.Wakilan Komitin sulhu na MDD su 15, sun yi wani taro jiya littini a New York na Amirca, inda suka yi wasu gyare-gyare a kudirin nasuda zasu gabatar wannan makon gameda yadda zaa bullowa kasashen na Sudan biyu.Kasar China wqadda kawa ce ta Sudan ta kudu da Sudan kanta, ta nuna bata kaunar kasar Amirka da kasashen Yammaci su malkayawa sudan wani takunkumi, ita kuma Russia ta nuna itama tana goyon bayan China.