Mali

Sanogo yace sun samu nasarar dakile yunkurin juyin mulki a Mali

Sojojin Mali a Hedikwatarsu a Kati, dake wajen birnin  Bamako
Sojojin Mali a Hedikwatarsu a Kati, dake wajen birnin Bamako Reuters/Luc Gnago

Kaftin Sanogo Jagoran dakarun Sojin Mali da suka hambarar da Tsohon shugaban kasa  Amadou Toumane Toure, yace sun yi nasarar dakile yunkurin juyin mulki da dakarun da ke goyan bayan tsohon shugaban suka yi a daren jiya.

Talla

An kwashe daren jiya ana musayar wuta a kafafen yada labaran Mali da Filin saukar jirgin sama tsakanin dakarun gwamnati da Sojojin Mali masu yunkurin juyin mulki.

Akwai mutane da dama da Kaftin Sanogo suka cafke bayan kafa gwamnatin rikon kwarya, matakin da ya yi sanadiyar samar da wani sabon rikici a kasar.

Sai dai Kaftin Sanogo ya fito a kafar Telebijin yana cewa dakarun shi sun karbe ikon kafafen yada labaran kasar da Filin saukar Jirgin sama.

A ranar 22 ga watan Maris ne Kaftin Sanogo ya jagoranci Juyin Mulki da suka hambarar da gwamnatin Amadou Toumani Toure.

Bayan matsin lamba daga kasashen duniya ne Sojin mali suka kafa gwamnatin rikon kwarya a ranar 12 ga watan Afrilu.

A ranar Assabar Kaftin Sanogo ya yi watsi da kudirin kungiyar ECOWAS game da tura dakarunta cikin Mali domin tabbatar da ganin gwamnatin kasar ta dawo hannun farar Hula.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.