Najeriya

Harin This Day: Boko Haram ta yi gargadin sake kai wa kafafen yada labarai hari

Harin Ginin Kamfanin Jaridar thisday a Abuja Najeriya bayan kai hari
Harin Ginin Kamfanin Jaridar thisday a Abuja Najeriya bayan kai hari REUTERS/Afolabi Sotunde

Kungiyar Jama'atu Ahlus Sunnah Lidda'awati wal Jihad da aka fi sani da sunan Boko Haram a Najeriya, ta fitar da Wani hoton Bidiyo mai dauke da bayanin harin Ofishin Jaridar This Day tare da yin barazanar ci gaba da kai wasu hare hare a manyan kafafen yada labarai da ma'aikatansu a kasar.

Talla

Sakon Bidiyo ya fara ne da Waka: “ Mu ba ‘Yan Boko Haram ba ne Sunanmu ‘Yan Najeriya, Mu musulmi ne, Ahlussunnah ku fadi gaskiya”.

Hoton bidiyon ya nuna yadda aka kai harin Ofishin Jaridar This Day tare da bayanin dalilan da yasa Kungiyar ta kai harin.

Shugaban kungiyar Imam Abubakar Shekau yace sun kai hari ne a Ofishin Jaridar This Day saboda amfani da Jaridar wajen yada batanci ga Annabi SAW a lokacin da aka yi bukin sarauniyar Kyau a birnin Kaduna a shekarar 2002.

Shekau yace Jaridar Thisday ta buga labarun karya game da kungiyarsu.

A cewar Shekau sun amsa wa Jaridar ba su ne suka yi garkuwa da Turawa ba a Sokoto amma Jaridar ta wallafa labarin sun dauki alhakin al’amarin kuma hakan karya ne Jaridar ke masu.

Kungiyar ta raba kafofin yada labarai zuwa gida ukku, inda ta ce gidan Jaridar Thisday shi ne kan gaba, sai Wasu Jaridu a Najeriya da suka hada da jaridar Punch da Jaridar Daily Sun da Vanguard da Guardian da Jaridar The Nation da Jaridar National Accord, sai kuma Muryar Amurka VOA Hausa da kungiyar tace zata kai wa Ofishinsu hari a kowane lokaci saboda abun da kungiyar ta ce shirye-shriyen da VOA suke yi kira ne ga jama'a domin tona asirinsu tare da ba Gwamnati goyon baya.

Imam shekau ya yi gargadi ga Kafar yada Labaran Sahara Reporters wadanda ke yada labarai a Intanet inda yace ana amfani da kafar wajen cin mutuncin addinin Musulunci don haka idan basu gyara aikin su ba zasu kaddamar masu da hari.

Bayan haka, kungiyar ta ja kunnen wasu kafafen yada labarai da tace suna dab da fadawa rukunin wadanda za su kai wa hari idan ba su yi hattara ba.

Kafofin yada labaran sun hada da, jaridar Leadership da Jaridar Daily Trust da kuma sashen Hausa na Radiyon Faransa, RFI.

Imam Shekau ya yi gargadi ga Gwamnati inda yace matukar gwamnati ba ta dai na kame matansu ba da yara, da rusa musu gidaje, to za su ci gaba da rusa gine-ginen gwamnati musamman makarantu.

Kalaman Shekau sun nuna kungiyar ta dauki alhakin kai harin Jami’ar Gombe da Jami’ar Bayero a Kano inda mutane da dama suka mutu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.