Congo-Kinshasa

Janar Jean Basco Ntaganda, ya musanta zargin cewar, yana da hannu a cikin fadan da aka gwabza a yankin gabashin kasar jamhuriyar demokradiyar Congo.

Le général Bosco Ntaganda, recherché par la Cour pénale internationale.
Le général Bosco Ntaganda, recherché par la Cour pénale internationale. © CPI

Janar Ntaganda ya musanta zargin saka hannunsa cikin mummunan fadan da aka gwabza a yankin gabashin Jamhuriyar Demokradiyar Congo, tsakanin dakarun kasar da wani gungun tsohin yan tawayen, da ya taba zama babban Hafsansu.Har ila yau, Ntaganda ya musanta cewa yana da hannu a cikin korar wasu sozoji da gwamnatin kasar ta yi.Tun ranar lahadin da ta gabata ne dai, wani mummunan fada ya barke a yankin arewacin Kivu, wanda yayi sanadiyar saka yan kasar ta Congo dubu 2 mafi yawansu yara, suka yi hijira zuwa cikin kasar Rwanda mai makwabtaka da kasar ta JDC.