Senegal-kamun kifi
A kasar Senegal masuntan kasar sun gamsu da soke lasisin iznin yin Suu ga masuntan kasashen waje.
Wallafawa ranar:
A ranar litanin da ta gabata ne, gwamnatin kasar Senegal ta bayyana soke Lasisin iznin yin Suu da aka baiwa masunta kasashen waje a kasar.Shekaru biyun da suka gabata ne dai, gwamnatin kasar ta Senegal da ta gabata ta baiwa jiragen ruwan masuntan kasashen turai iznin yin Suu a kan dalar Amruka 15 kowane Ton na kifi, al’amarin da masuntan kasar ta Senegal suka nuna matukar bacin ransu a kansa, mataki da a cewarsu ke barazana ga sana’ar tasu ta Suu.Wannan sabon mataki da gwamnatin Macky Sall ta dauka, ya sanyayya zukatan Masuntan dangane da barazanar da sana’ar tasu ke fuskanta.