Libya-kotun duniya

Lbiya ta bukaci ICC ta tsame hannuta daga shari'ar da za'a yi wa Saiful Islam

daga gaba a dama Moustapha Abdeljalil shugaban kasar Libiya a hagu  Luis Moreno Ocampo mai shigar da karar kotun duniya
daga gaba a dama Moustapha Abdeljalil shugaban kasar Libiya a hagu Luis Moreno Ocampo mai shigar da karar kotun duniya Reuters/Ismail Zitouny

Gwamnatin kasar Libiya a hukumance ta kalubalanci kotun duniya cewa, bata da hurumin hukumta dan tsohon shugaban kasar Marigayi Ma’ammar Kadhaf, Seiful Islam, da kuma tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar Abdallah al Sanusi.Yanzu haka dai, Saiful Islam na tsare ne ga hannu mahukumtan juyin juya halin kasar ta Libiya ne a garin Zenten, a yayin da Aballah al Sanusi ke tsare a kasar Moritaniya bayan kama shi, kotun duniya na bukatar gurfanar da su a gabanta ne, bayan da ta bada samacin kamo mata su a shekarar da ta gabata, bisa zarginsu da aikata laifukan cin zarafin bil’adama. Kafin samun abinda ta ke so, gwamnatin kasar Libiya na bukatar gabatar wa alkalan kotun duniyar bukatarsu a rubuce domin tsame hannunta daga shara’ar ta mutanen 2, abinda tuni mahukumtan na Libiya suka yi a jiya talata 1 ga watan Mayu shekara ta 2012, inda yanzu suke cikin jiran amsar da zata biyu bayan bukatar da suka gabatar.