Sharhin Jaridu

Sharhin wasu Jaridun duniya da Afrika

Les manchettes des journaux ivoiriens commémorent ce 11 avril 2012, à leur manière,  l'arrestation de Laurent Gbagbo, il y a un an jour pour jour.
Les manchettes des journaux ivoiriens commémorent ce 11 avril 2012, à leur manière, l'arrestation de Laurent Gbagbo, il y a un an jour pour jour. © Sia Kambou/AFP

URUGUAY DAILY NEWS……Ta buga labarin damke ‘yan fursuna 70 bisa zargin mallakar makamai da miyagun kwayoyi a cikin Kurkuku.To shine gwamnatin kasar ta Uruguay ta bayyana cewar yanzu bata amincewa Gandurobobin dake aiki a gidajen kason ba, abinda ya kaita ga neman izni ga majalisar kasar kan bukatar samar da jami’an soji 600 da zasu rinka sa Ido ga gidajen kaso 28 daga sassa daban-daban na kasar.Wannan kuwa saboda acewar su, sun fahimci cewar shiga da makamai da miyagun kwayoyi a gidajen kaso, bai rasa nasaba da cin hanci da rashawa a gidajen kason.DAILY INDEPENDENT CALPONIA…..Ta buga labarin wani mutum mai suna Brayan Klassen da kotu ta cajeshi da laifin soke wani matashi da Wuka har ya mutu.An dai ga yaron da aka kashe dan shekara 21 ne kwance cikin jini da alamun sukar Wuka a saman kuibin sa na Hugu.SAUDI GAZETTE….Ta buga labarin cewar kasar Su’udiyya zata samar da gurabun ayyukan yi ga ‘yan kasar har 8000 a sashen kula da sauka da tashin jiragen sama na kasar.Muhammad Al Zeer, shugaban hukumar kula da sauka da tashin jiragen saman ta MAZ Aviation a kasar ta Saudiyya, yace dama masarautar kasar ta saudiyya ta ware Riyal miliyan dubu 200 domin samar da cigaba a fannin na kula da sauka da tashin jiragen sama a kasar ta Saudiyya.Kuma hukumomin kasar, sun tabbatar da cewar a cikin watan Nuwamba ne za’a fara aikin fadada babban filin jirgin Riyadh.VIBE GHANA….Ta buga wani labari mai ban tausayi kan wani yaro matashi dan shekara 15 mai suna Idirisu Abubakar da Wutar lantarki ta kamashi ya kuma mutu.Al’amarin dai ya auku ne a wani kauye da mafi yawancin mazaunan sa manoma ne.Jami’an ‘yan sanda dai sun sanar da cewar Wutar ta kama Idirisu ne a lokacin da yake kokarin dosana Soketin Talabijin da yariga ya lalace, kawai sai wutar ta kamashi.AMINIYA NAJERIYA…..Ta buga labarin wani jami’in dan sanda a birnin Minna ta jihar Niger, daya make dan kabu-kabu, ko Achaba da Katako, kuma yace ga garin ku.Dan acaban mai shekara 28 zuwa 30, ya baro Unguwar Mandela ne yana hanzarin zuwa cikin gari, sai ya hango wani dan sanda a daidai mahadar Sauke-Ka-HutaHango dan sandan ne ya sa dan acaban ya juya kan babur dinsa wai don ya tsira, bai sani ba akwai wani dan sanda cikin farin kaya da ke rike da katako a hannu wanda bai bata lokaci ba, kawai ya buga masa shi aka, yace ga garin ku.Ganin aukuwar wannan lamarin ne ya sa mazauna yankin suka yi caa! akan dan sandan suka cafke shi kuma suka lashi takobin aikawa da shi Lahira, kamar yadda ya yi wa dan acaban da suka nuna bai aikata wani laifin da aka kashe shi ba.KOSAVO PRESS…Ta buga labarin cewar al’ummar kasar na koken yadda a wasu sassan kasar aka kwashe fiyeda sa’o’I 16 ba hasken Wutar Lantarki.Hakama inji jaridar an damke wasu mutane dauke da Ton 2 na tabar WIWI, a yayinda aka kashe mutum 1 aka kuma jikkata da dama, ‘yan sanda dai sun kama wadanda ake tuhuma su 2.NATIONAL MIRROR NIGERIA….Ta buga labarin wani tsohon ma’aikacin bankin fisrt Back a birnin Lagas na tarayyar Najeriya da kotu ke tuhuma da aikata laifuka 3 na farko shine hada baki a aikata laifi, damfara, da kuma sata.Tsohon ma’aikacin dai ya damfari mutane masu hulda da bankin na first Bank kudi naira miliyan 13 bayan Bankin ya riga ya koreshi daga aiki tun a shekarar 2009.Amma kuma ya cigaba da amsa sunan ma’aikacin Bankin inda yayi ta yaudarar mutane kudi makuddai ba’a ahama ba har sai da suka kai fiyeda naira miliyan 13.