Mali-Alkaida

wata kungiyar alka'ida a kasar Mali ta nemi biyan diyya kafin ta sako wasu mata turawa guda 2

wasu yan tawayen Abzinawan kasar Mali
wasu yan tawayen Abzinawan kasar Mali

A kasar Mali Wata kungiya dake da halaka da kungiyar Al-Qaeda, ta nemi a bata kudin daya kai kudin Turai Euro Miliyan 30 kafin su sako wasu turawa biyu da suke garkuwa dasu.Mai Magana da yawun kungiyar ta Movement for Oneness and Jihad in West Africa, ta hannun kakakin kungiyar Adnan Abu Walid Sahroui, yace idan an bada wadannan kudade zasu saki mutanen da suke garkuwa dasu.Turawan duka mata ne, su biyu, ‘yar kasar Italia da kuma ‘yar kasar Spain, wadanda suke aikin agaji, a sansanin ‘yan gudun hijira dake garin Tindouf dake yammacin kasar Algeria.