Sudan-Sudan ta Kudu
Kasar Sudan ta Kudu ta ce Sudan ta arewa ta kai mata hari ta sama
Wallafawa ranar:
Sozojin kasar Sudan ta kudu sun zargin Kasar Sudan ta Arewa da yin ruwan wuta ta sama, tare da harba makaman Atilare a cikin yankunan Sudan ta kudu, kusa da kan iyakokin kasashen guda 2, duk kuwa da gargadin kakaba takunkumi da komitin tsaro na MDD ya yi, idan kasashen 2 sun ci gaba da yin tashin hankali a tsakaninsu.Kakakin rundunar sojan kasar Sudan ta kudu Philip Aguer, ya bayyana cewa, jiragen yakin kasar ta Sudan sun yi ruwan bama bamai, tare da na makaman Atilare a sansanin SPLA, wanda hakan ke nufin share fage ga kai hare hare ta kasa