Masar

Mutane 20 suka mutu a zanga-zangar kin jinin Sojin Masar

Masu zanga-zanga a kasar Masar
Masu zanga-zanga a kasar Masar KHALED DESOUKI / AFP

fiye da mutune 20 ne suka mutu a zanga-zangar kin jinin Soji da aka gudanar a birnin Alkahira na kasar Masar. Akan haka ne ‘Yan takarar shugabancin kasar 4 suka bayyana dakatar da gangaminsu sakamakon mutuwar mutanen.

Talla

Zauna-Gari-Banza ne suka afkawa masu zanga-zangar kin jinin Soji a kusa da ma’aikatar tsaro a birnin Alkahira.

taho-mu-gamar dai ta yi sanadin mutuwar akalla mutum 20 koda yake alkalumma na cewa wadanda suka mtu sun wuce haka.

Tsohon shugaban gamayyar kasashen larabawa Anwar Musa, yace kashe-kashen nada manuniyar akan al’ummar kasar sun kagara samun sabuwar gwamnatin Demukradiyya.

Rundunar Sojin kasar ta sanar da cewa ta shiryawa mika mulki ga zababben shugaba ranar 24 ga watan Mayu idan aka kammala zaben a zagaye na farko.

Ko a ranar Lahadi sai da aka kashe mutum daya tare da raunata wasu 119 a fito-na-fito tasakanin magoya bayan Abu Isma’il da kuma mazauna Abbasiyya.

Zanga-zangar ta haifar da tayar da zaune tsaye, abinda ya dankwafar da farinjinin shugaba Husni Mubarak a shekarar data gabata, ta rikide zuwa tashin hankali, da ‘yan ta’adda masu neman ta kife.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.