Libya-kotun duniya

yar tsohon shugaban kasar Libiya Marigayi Ma'amar Kaddafi ta nemi a yi binciken yadda aka kashe mata uba

Le corps du guide libyen, Mouammar Kadhafi  le 21 octobre 2011, à Misratra.
Le corps du guide libyen, Mouammar Kadhafi le 21 octobre 2011, à Misratra. REUTERS/Saad Shalash

‘Yar marigayi Moammar Gaddafi na kasar Libya, Aisha Gaddafi ta nanata bukatar ganin Hukumomin fadin duniya sun tallafa mata tilasta binciken yadda aka kashe mahaifinta da wani dan-uwanta dake tare da mahaifin nata.Aisha Gaddafi wadda ta tafi kasar Algeria, tun watan Augusta na shekarar data gabata ta nemi kotun kasa da kasa dake hukunta masu aikata manyan laifukan yaki da su yi wani abu game da wannan lamari.Aisha Gaddafi ta nemi Komitin sulhu na MDD da ya yi abinda ya kamata gameda bukatar tata.