Jamhuriyyar Congo

Dakarun Congo sun ce sun isa mafakar Ntaganda da ake nema ruwa a jallo

Janar Bosco Ntaganda,
Janar Bosco Ntaganda, AFP

Dakarun Sojan kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo, sun ce sun isa, zuwa maboyar gudajjen janar din sojan kasar Jean Bosco Ntaganda, da ake zargi da haddasa tashin hankalin da ya yi sanadiyyar dubun dubatan mutane rasa gidajensu.

Talla

Wani Kanar na Soja ya shaida wa kamfanin dillacin labarun kasar faransa AFP cewa an gwabza fada tsakanin sojoji masu biyyya ga gwamnati da mabiya Ntaganda a kusa da birnin Goma.

MajalisarDinkin Duniya tace kimanin mutane dubu 20 ne suka tserewa fada da ya barke a ranar Lahadi, Wasu dubu Hudu kuma suka ketare daga kasar zuwa Rwanda.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.