Najeriya

Gwamnatin Flato a Najeriya ta haramta yin Acaba

'Yan Acaba a Najeriya
'Yan Acaba a Najeriya The News Africa

Gwamnatin Jahar Flato a Najeriya ta sanar da haramta yin Acaba da babura a birnin Jos da kewaye, saboda yunkurin dakile ayyukan laifi da ake da baburan, kamar yadda ta sanar bayan taron Majalisar zartaswan Jahar, tare da jaddada cewa dokar ta fara aiki nan take.

Talla

Rediyo Faransa ya yi kokarin jin Tabakin Gwamnatin Jahar musamman kwamishinan yada labaran Jihar, Abraham Yiljap, amma yace Gwamnatin Jiha ta kammala shirin aiwatar da dokar yanzu Magana tana hannun jami’an tsaro.

Sai dai kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Emmanuel Ayeni, yace kuskure ne, babu gaskiya game da batun amma Kwamishinan bai karin haske ba akan batun.

Tuni dai ‘Yan Acaba masu hayar babura, da ma masu hawa na kashin kansu, suka fada cikin zullumi bayan sanar da dokar, wanda ake ganin zata jefa dubban mutane cikin halin kakani-kayi saboda rashin ayyukan yi.

Matasa a Najeriya na fuskanta kalubalen rashin aikin yi a kasar al’amarin da yasa masana ke ganin rashin aikin yi ne ke kawo tashe tashen hankula da ayyukan ta’addanci a Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.