Najeriya

Gwamnatin Jahar Legas a Najeriya ta kori Likitoci 788

Likitocin Najeriya a Jahar Legas lokacin da suke maci domin neman biyansu kudaden Albashi
Likitocin Najeriya a Jahar Legas lokacin da suke maci domin neman biyansu kudaden Albashi Reuters

Hukumomin Jahar Legas a Najeriya sun tabbatar da sallamar Likitoci 788 wadanda ke yajin aiki tsawon makwanni uku. Gwamnatin Jahar Legas tace yajin aikin Likitocin ya sabawa doka.

Talla

Wata Sanarwar da Gwamnatin Jahar ta fitar  tace matakin sallamar Likitocin ya biyo bayan kasa amsa dalilin da yasa suka karaucewa aiki ba tare da izini ba karkashin dokar aiki.

Yanzu haka Gwamnatin Jahar ta dauki Likitoci 373 domin maye gurbinsu.

Daruruwan mutane ne dai suka gudanar da zanga-zanga a Ofishin Gwamnan Jahar Babatunde Bashola saboda halin da suka shiga sanadiyar yajin aikin Likitocin.

Sai dai Likitocin sun shiga yajin aikin ne saboda neman karin Albashi  da wasu kudaden lada.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.