Nijar-Save the Children

Nijar ta yi watsi da rahoton Save The Children akan Mata

Jerin Mata masu shayarwa a Nijar suna jiran Likita
Jerin Mata masu shayarwa a Nijar suna jiran Likita

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yi watsi da rahotan kungiyar agaji ta Save the Children, wanda yace mata na fama da tsananin wahala wajen haihuwa da kuma renon kananan yara, abinda ya sa kasar ta zama ta karshe a mizanin kasashen duniya 165.

Talla

Ministan kula da kyautata rayuwar mata da kananan yara Khadijatu Dan Dobi tace wata kila kungiyar ta yi amfani da mizanin shekarun baya lokacin da damina ba ta yi kyau ba a bara amma ta ce yanzu akwai ci gaba da aka samu.

Wannan dai ya biyo bayan wani sabon Rahoto game da halin rayuwar iyaye mata da hukumar kare lafiyar kananan yara ta fitar, inda Rahoton ya nuna Nijar ce kasar da iyaye Mata ke shan wahala bayan maye gurbin kasar Afghanistan a karon farko. Kasar Norway ce a matsayin kasa ta farko da iyaye Mata ke shan dadi a jerin kasashe 165 da aka kwatanta rayuwarsu.

Kungiyar karelafiyar kananan yara "Save The children" ta yi la’akari ne da matsalolin da suka shafi kiwon Lafiya da karancin Ilimi da rashin samun abinci mai gina jiki da kuma tattalin arziki.

Hukumar tace matsalar karancin Abinci da ke addabar yankin Sahel ita ce ke barazana ga rayuwar Miliyoyan kananan yara a yankin.

Rehoton kungiyar Save the children yace rashin samun abinci mai gina jiki shi ne ke haifar da yawan samun mace macen mata da kananan yara a wajen haihuwa.
Hukumar ta yi gargadin cewa idan uwa bata da isassar lafiya da rashin wadataccen ilimi tare da yin ayyukan wahala zai hana ta shayar da Jariri yanda ya dace.

kungiyar tace hanya mafi sauki ta magance matsalar rashin Abinci mai gina jiki tsakanin Uwa da jaririnta ita ce kula da kwanaki 1,000 na farko tun daga samun ciki.

Kungiyar ta yi kira ga shugabannin duniya domin gaggauta daukar mataki wajen magance matsalar yawan mace macen mata da rashin abinci mai gina jiki a taron kasashen G8 da za’a gudanar nan da makwanni biyu.

Kasar Guinea Bissau da Mali da ke fuskantar rikicin siyasa sune a matsayin kasashe na hudu dana Biyar da rayuwar mata ke cikin mawuyacin hali bayan Afghanistan a matsayi na Biyu sai kasar Yemen a matsayi na uku.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.