Libya

An yi musayar Albarussai tsakanin ‘Yan bindiga da jami’an tsaron Libya

'Yan tawayen Libya rike da muggan makamai a lokacin yaki da dakarun Marigayi Gaddafi
'Yan tawayen Libya rike da muggan makamai a lokacin yaki da dakarun Marigayi Gaddafi

A kasar Libya mutane da dama sun samu rauni tare da samun mutuwar mutum daya sakamakon musayar wuta da aka yi tsakanin Jami’an tsaro da ‘Yan bindiga dwadanda suka yi zanga zanga a Hedikwatar Gwamnati a Birnin Tripoli.

Talla

Rahoranni sun ce, ‘Yan bindigan sun fito ne daga garin Kafran, inda suka bukaci kudade daga ofishin Fira Ministan, al’amarin da kuma ya rikide ya koma tashin hankali.

Adel Osman, kakakin ma’aikatar tsaro, yace mutane da dama sun mutu, wasu kuma sun jikkkata.

Yanzu haka Khaled Besher shugaban kwamitin tsaro a Tripoli yace an cafke mutane 14 cikin ‘Yan bindigar.

Tun da farko dai gwamnatin kasar ta fara biyan ‘Yan tawaye kudade kafin daga bisani aka dakatar da biyansu, al’amarin day a fusata wasunsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.