ECOWAS-Guinea Bissau-Najeriya

ECOWAS zata tura Tawaga zuwa G/Bissau, inji Goodluck

Shugaban Cote d'IVoire Alassane Ouattara kuma shugaban ECOWAS a lokacin da yake ganawa da Goodluck Jonathan na Najeriya a filin saukar jirgi na Felix Houphouet Boigny a Abidjan
Shugaban Cote d'IVoire Alassane Ouattara kuma shugaban ECOWAS a lokacin da yake ganawa da Goodluck Jonathan na Najeriya a filin saukar jirgi na Felix Houphouet Boigny a Abidjan REUTERS/Luc Gnago

A wata ziyara da kai kasar Cote d’Ivoire, Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, yace kungiyar kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, zata tura wata tawaga zuwa kasar Guinea Bissau don tattaunawa da sojojin kasar, domin ganin sun mayar da kundin tsarin mulki.

Talla

Shugaban ya fadi haka a lokacin da yake ganawa da shugaban Cote d’Ivoire Alassane Ouattara.

A yau Alhamis ne ake saran tawagar zata isa zuwa Guinea Bissau, don tattauna yadda za’a girke dakarun da zasu taimaka wajen ganin an mayar da mulki ga fararen hula.

Ana ci gaba da zama cikin fargaba a kasar Guinea Bissau tun bayan da Sojoji suka karbe iko a ranar 12 ga watan Afrilum, al’amarin da ya wargaza zaben shugaban kasa.

Tuni dai Jonathan nufi taron tattalin arzikin Africa a Addis Ababa bayan ya ficewa Cote d’Ivoire.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.