Algeria

Zaben ‘Yan Majalisa a Algeria

Wasu mata suna tafiya kusa da hutunan 'Yan siyasa da aka lika a bangon a birnin Algiers.
Wasu mata suna tafiya kusa da hutunan 'Yan siyasa da aka lika a bangon a birnin Algiers. REUTERS/Zohra Bensemra

Al’ummar Algeria sun fara kada kuri’arsu a zaben farko na ‘Yan Majalisu tun fara zanga-zangar kasashen Larabawa, inda Jam’iyyar Mai mulki da Jam’iyyar ‘yan uwa musulmi ke fatar samun rinjayen kujeru tsakanin Jam’iyyu 44 da suka shiga takarar zaben ‘Yan Majalisa 462.

Talla

Da misalin karfe 7:00 Agogon GMT aka fara bude runfunan zabe a manyan biranen kasar cikin tsauraran matakan tsaro.

Jam’iyyun siyasa 44 ne suka shiga takarar zaben, amma 21 cikinsu sabbin Jam’iyyun Siyasa ne.

A Watan Janairun bara ne Zanga Zanga ta barke a kasar Algeria lokacin da Al’ummar Larabawa suka kaddamar da Juyin Juya hali a yankunansu, amma shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika ya yi kokarin kwantar da zanga zangar inda ya yi wa tsarin Demokradiyyar kasa kwaskwarima tare da karin albashi ga ma’aikata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.