Algeriya

Jam,iyar RCD a kasar Aljeriya ta ce kashi 18% na masu zabe ne suka halarci zaben jiya alhamis

Plus de 21 millions d'Algériens se rendent aux urnes ce jeudi 10 mai pour élire leurs députés.
Plus de 21 millions d'Algériens se rendent aux urnes ce jeudi 10 mai pour élire leurs députés. Reuters/Louafi Larbi

Jamiyar RCD da ta kauracewa zaben yan majalisar dokokin da aka gudanar a jiya alhamis a kasar Aljeriya, ta kalubalanci sakamakon da gwamnatin kasar ta bayar, kan yawan jama’ar da suka halarci zaben na kashi 42,9%, inda ta ce sakamakon bai wuce kashi 18% ba, kamar yadda shugaban jami’iyar Mohcin Bellabas ya sanar.A lokacin wani taron manema labarai da ya kira a yau juma’a a birnin Alger babban birnin kasar, M. Bellabas ya bayyana cewa, sakamakon wadanda suka halarci zaben da kwamitin da ke kula yankunan kasar ya bayar kafin gwamnati ta canza shi bai wuce 18% ba.