MDD-Sudan

Ban Ki-moon ya bukaci Sudan janye Dakarunta daga Abyei

Dakarun Sudan a yankin Heglig daya daga cikin yankunan da ake rikici tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu
Dakarun Sudan a yankin Heglig daya daga cikin yankunan da ake rikici tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu Photo AFP/ Adriane O’Hanesian

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya bukaci Sudan ta janye dakarun ta daga Yankin Abyei da ake takaddama akai. Ban wanda yake jawabi bayan ficewar dakarun Sudan ta kudu, ya bukaci kasashen biyu su mutunta yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.

Talla

A bangare daya kuma, shugaban hukumar kula da ‘Yan gudun hijira na kasar Sudan, Jill Helke, ta koka kan halin da dimbin ‘Yan gudun hijirar Sudan ke ciki.

Helke tace kashi na farko sun hau jirage uku zuwa Juba, kashi na biyu zasu bar Khartoum dan kwashe wasu mutane 400.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.