Uganda

An cafke wani jagoran ‘Yan tawayen LRA a Uganda

Caesar Acellam
Caesar Acellam REUTERS/James Akena

Hukumomin Kasar Uganda sun ce, sun yi nasarar kama Caeser Acellam wani babban kusa a kungiyar ‘Yan Tawayen Lords Resistence Army, da ke karkashin Joseph Kony. Kakakin rundunar sojin Uganda, Lt Col Felix Kulayigye, yace Acellam ne jami’I na hudu a kungiyar ‘Yan Tawayen, bayan Joseph Kony, da Dominic Ongwen da Okot Odhiambo.