ECOWAS-Guinea Bissau-Najeriya

Najeriya zata tura dakarunta zuwa Guinea Bissau

Taswirar kasar Guinea Bissau da kasashen da ke makwabtaka da kasar
Taswirar kasar Guinea Bissau da kasashen da ke makwabtaka da kasar Anthony Terrade/RFI

Gwamnatin Najeriya tace zata girke dakarunta a kasar Guinea Bissau don taimakawa kasar komawa ga mulkin fararen hula, kamar yadda kungiyar ECOWAS ta bukata.Ministan tsaron Najeriya, Dakta Bello Halliru yace Najeriya ta karbi kira ne daga kungiyar ECOWAS domin samar da tsaro a kasar Guinea Bissau.

Talla

A cewar Mista Halliru, Najeriya bata da niyyar aika Sojoji a wata kasa sai idan an gayyace ta don taimakon Majasalisar Dinkin Duniya ko kungiyar ECOWAS.

A makon jiya ne Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, yace kungiyar kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, zata tura wata tawaga zuwa kasar Guinea Bissau don tattaunawa da sojojin kasar, domin ganin sun mayar da kundin tsarin mulki.

Shugaban ya fadi haka a lokacin da yake ganawa da shugaban Cote d’Ivoire Alassane Ouattara.

Ana ci gaba da zama cikin fargaba a kasar Guinea Bissau tun bayan da Sojoji suka karbe iko a ranar 12 ga watan Afrilum, al’amarin da ya wargaza zaben shugaban kasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.