Najeriya

Hisbah ta daura auren Zawarawa 100 a Kano

Gungun mata da Amaren da aka daurawa aure a Kano
Gungun mata da Amaren da aka daurawa aure a Kano Tasiu Kano

Hukumar Hisbah a Jihar Kano, ta daura wa Zawarawa 100 aure cikin 1,000 da aka shirya yi, dan magance mace macen aure a Jahar. Kuma Hukumar Hisbah tace ta dauki alhakin gudanar da bikin ne a madadin gwamnatin Jiha.

Talla

An gudanar da daurin auren ne a fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Dakta Ado Bayero, wanda ya samu halartar dubban mutane.

Wakilinmu a Kano, Muhammad Tasiu Lawal yace gwamnatin Jahar Kano said a ta samar da kudi Naira miliyan Goma Sha shida domin gudanar da gagarumin Bukin. Kuma Sheikh Isiyaka Rabiu ne ya ba Angwayen Sadakin kudi Naira Dubu Goma.

Maitaimakin kwamanda Hisba Malam Yakubu Mai gida Kacako yace sun yi kokarin hada auren ne ta hanyar idan Mace tana da masoyin da take so ta gabatar da shi, idan kuma bata da wanda take so sai ta bayar da sunanta domin samar mata wanda ya dace da ita karkashin Shari’a.

Akwai dai Walima da hukumar Hisbah ta shirya wa ma’uratan domin samun albarkar auren.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.