MDD-Afrika

Sai an Magance Yunwa kafin a samu ci gaba a Afrika, Inji MDD

Wani manomi a yankin kasar Chadi
Wani manomi a yankin kasar Chadi AFP PHOTO / OXFAM / IRINA FUHRMANN

Hukumar Ci gaba ta Majalisar Dinkin Duniya, tace dole sai kasashen Afrika sun magance matsalar yunwa da ke addabar kasashe 27 a nahiyar kafin kasancewa matsayin Yankin da ya samu ci gaba.

Talla

Tattalin arzikin nahiyar Afrikan dai na karuwa ne da maki Biyar a shekaru Goma da suka gabata, amma yanayin bunkasar tattalin arzikin Nahiyar baya tabuka wani abin azo a gani musamman wajen magance matsanancin talauci da ke addabar Nahiyar, inji Hukumar.

Mai bai wa hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya shawara akan Afrika, Sebastine Levin, yace alamun samun nasara a kadan ne domin bunkasar tattalin arzikin kasashen.

Shi kuma babban masanin tattalin arziki na hukumar, Pedro Conceicao, yace muddin ba a magance matsalar rashin abinci ba to wannan bunkasar tattalin arzikin da ake gani a nahiyar ba zai dore ba.

Nahiyar Afrika ita ce ta biyu bayan Nahiyar Asia ta fuskar bunkasar tattalin arziki a duniya amma kuma fiye da kashi 48 na mutanen nahiyar na cikin tsananin talauci.

Har ila yau, Afrika kan shigo da abinci da yawa daga kasashen ketare duk da cewa tana da kasar noma da kuma isasshen ruwa..
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.