ECOWAS-Guinea Bissau

Dakarun hadin gwiwa na kasashen afrika ta yamma za su fara sauka kasar Guinea Bissau a gobe Juma’a a

Photo de famille de la Cédéao avant le début du sommet à Dakar consacré à la crise en Guinée-Bissau et au Mali, le 3  mail 2012.
Photo de famille de la Cédéao avant le début du sommet à Dakar consacré à la crise en Guinée-Bissau et au Mali, le 3 mail 2012. AFP PHOTO / Seyllou

Dakarun hadin gwiwa na kasashen afrika ta yamma za su fara sauka kasar Guinea Bissau a gobe Juma’a a dai dai lokacin da ake wa kasar Mali kashedin kakaba mata takunkumi muddin bata koma kan tafarkin demokradiya ba.  

Talla

Sanarwar tura dakarun hadin gwiwar na kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS ko CEDEAO, wacce ta fito a yau, ta bayyana cewa, za’a tura dakaru dari shida da ishirin da tara zuwa kasar ta Guinea Bissau domin su tarbi sojojin kasar Angola wajen mayar da mulkin farar hula a kasar.

An dai fitar da wannan sanarwar ce bayan wani taron manyan kusoshin jami’an tsaron na yankin, a lokacin da a ke sa ran sojojin na Angola za su fice a ranar 30 ga watan Mayun nan.

Su dai sojojin kasar ta Guinea Bissau in ba’a manta ba, suna zargin gwamnatin farar hular kasar ne da hada kai da sojojin na Angola don a muzguna musu, wanda hakan ya sa su ka kifar da gwamnatin

Har ila yau kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO ta ce ta na nan tana shirya akalla sojoji 3,000 wanda za ta tura kasar Mali, wacce akayi juyin mulki a watan Maris na wannan shekara, ta na mai jaddada cewa jira kawai ta ke yi hukumomin na Mali su gayyacesu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.