Afriaka ta kudu-Gabon

Jacob Zuma na Afrika ta kudu yace kasar sa ba zata yi wa kasar Gabon fin karfi ba

Jean Ping et Dlamini Zuma, en lice pour la présidence de la Commission de l'Union africaine.(Montage photo CC et AFP)
Jean Ping et Dlamini Zuma, en lice pour la présidence de la Commission de l'Union africaine.(Montage photo CC et AFP)

Shugaban kasar Africa ta kudu Jacob Zuma yace kasar sa ba zata yiwa kasar Gabon fin karfi ba wajen kokarin da suke yi na fidda sabon Shugaban Hukumar Kasashen Africa AU.Cikin watan Janairu na wannan shekarar dai Kasashen nahiyar sun kasa zaben Shugaban Hukumar Kungiyar tasu, tsakanin Shugaba mai ci Jean Ping wanda dan kasar Gabon ne dake rike da Mukamin tun 2008, da kumna ‘yar kasar Africa ta kudu Nkosa-zana, wadda kuma tsohuwar matar Shugaban Africa ta kudun ne.Koda a makon jiya Shugabannin nahiyar sunyi taro a kasar Benin domin duba lamarin, amma kuma bisa dukkan alamnu sai taro na gaba na kungiyar da zatayi a Malawi, cikin watan 7.