Kenya
mai shigar da karar Kotun duniya, ya nuna fargabarsa kan tsaron lafiyar masu bada shaida kan rikicin zaben kasar Kenya
Wallafawa ranar:
Babban mai shigar da kara na Kotun kasa da kasa, Luis Moreno Ocampo ya nuna fargaban sa game da lafiya shaidu na kasar Kenya da zasu bada shaida gameda tuhumar da ake yi wa wasu mutane 4 a kasar, na laifukan cin zarafin jama’a lokacin rikicin daya biyo bayan zaben kasar na 2007-2008.Farkon wannan shekarar ne dai, Kotun mai mazaunin ta a Hague ta yanke shawarar cewa, zata binciki zargin da akewa wasu manyan jamian Gwamnatin Kenya 4, na hannu waje kisan mutane a kalla 1,133 lokacin rikicin kasar shekaru 4 dasuka gabata.