Sudan-Sudan ta Kudu

Manzon kungiyar tarayyar Afrika kan rikicin kasashen Sudan Thabo Mbeki ya isa Khartum

Thabo Mbeki: «L'UA est très très engagée à faire en sorte que la paix soit  préservée en Côte d'Ivoire».
Thabo Mbeki: «L'UA est très très engagée à faire en sorte que la paix soit préservée en Côte d'Ivoire». AFP/ Kambou Sia

Mai shiga tsakani da Kungiyar kasashen Africa ta nada domin shawo kan takaddamar data kaure tsakanin kasar Sudan da makwabciyar ta Sudan ta kudu, wato Thabo Mbeki tsohon Shugaban kasar Afrika ta kudu, na kan hanyarsa ta zuwa Khartoum na kasar Sudan.Kasashen biyu dai sun ki bin umarnin Kungiyar kasashen Afrika na su daina fadan da suke yi, inda ake neman su koma kan kujeran sulhu.Ana saran Thabo Mbeki ya gana da Shugaba Omar al-Bashir da sauran jiga-jigan Gwamnatin kasar.