Mali-ECOWAS

Traore ya yi watsi da bukatar samar da shugaban wuccin gadi a Mali

Dioncounda Traore,Shugaban rikon kwaryar gwamnatin kasar Mali
Dioncounda Traore,Shugaban rikon kwaryar gwamnatin kasar Mali REUTERS/Malin Palm

Shugaban Gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali, Dioncounda Traore, ya yi watsi da bukatar sojin da suka yi juyin mulki a kasar, game da bukatar kiran taron kasa dan zaben shugaban wucin gadi.

Talla

Mista Traore yace matakin ba zai zama hanyar magance rikicin siyasar kasar ba, Bayan ganawa da shugaban kungiyar ECOWAS, Alassane Ouattara.

Kungiyar ECOWAS ta bukaci Traore ya jagorancin kasar na watanni 12 kafin gudanar da zabe.

Amma a ranar litinin ne Kaftin Sanogo jagoran Juyin mulki a kasar ya bukaci tattaunawa da gwamnatin riko domin samar da shugaban wuccin gadi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.