MDD-Sudan-Sudan ta Kudu

Wa’adin MDD game da sasanta rikicin Sudan ya kawo karshe

Dakarun Sudan
Dakarun Sudan AFP PHOTO / Hannah McNeish

A jiya Laraba ne wa’adin da Majalisar Dinkin Duniya ta diba domin kawo karshen rikicin Sudan da Sudan ta Kudu ya kawo karshe ba tare da cim ma maslaha ba tsakanin kasashen biyu. Sudan ta kudu ta zargi Sudan wajen kawo tsaikun sasantawar.

Talla

Pagun Amum mai jagorantan sansantawa daga bangaren kudancin Sudan yace kasar shi a shirye take ta koma teburin sasantawa da masu shiga tsakani na kungiyar Tarayyar Afrika.

A ranar 10 ga watan Afrilu ne Sudan ta balle daga zaman sasantawar bayan Kudancin Sudan ta larbe ikon yankin Heglig mai arzikin Man Fetir. Tun lokacin ne kuma sabon rikici ya barke tsakanin kasashen biyu.

Sai dai Sudan Ta Kudu tace nan bada dadewa ba, zata sayo makami mai linzami don kakkabo jiragen saman da Sudan ke amfani da su dan kai mata hari.

Kakakin sojin kasar, Kanal Philip Aguer, yace matakin ya zama wajibi domin kare kanta da al’ummarta, daga munana hare haren da ake samu a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.