Najeriya

Wasu Dattawan Arewacin Najeriya sun gana da Goodluck akan batun Boko Haram

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan,
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, REUTERS/Afolabi Sotunde

Tsohon Ministan Abuja Jeremiah Useni ya jagoranci wata tawagar dattijan Arewa inda suka gana da Shugaba Goodluck Jonathan akan batun hare haren bama bamai da ke addabar yankin Arewacin Najeriya.

Talla

Cikin wadanda suka rufa masa baya sun hada da tsohon gwamnan Katsina Sa’idu Barda da Tanko Yakasai da tsohon Sufeto na ‘Yan Sanda Ibrahim Komasi.

Jaremiah Useni yace sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi matsalolin da ke addabar Najeriya tare da yabawa da kokarin gwamnati wajen magance matsalar tsaro a kasar.

Mista Useni yace suna goyon bayan yunkurin sasantawa da Kungiyar Boko Haram domin kawo karshen zubar da jini.

 

Bayan kammala taron, Miniatan yada labaran Najeriya Labaran Maku yace Shugaban Goodluck Jonathan ya nuna damuwar shi ga kalaman Janar Muhammadu Buhari akan batun Boko Haram.

Amma a nata bangaren Jam’iyyar adawa ta ACN ta yaba da kalaman Buhari, inda take cewa idan gwamnatin PDP na shirin gudanar da sahihin zabe a shekarar 2015 to me zai sa gwamnati ta damu da kalaman tsohon shugaban.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.