Masar

Jam’iyyar Brotherhood ta hada gangamin masoya a Masar

Gangamin magiya bayan muhammed Mursi dan takarar shugabancin kasa karkashin tutar Jam'iyyar Brotherhood
Gangamin magiya bayan muhammed Mursi dan takarar shugabancin kasa karkashin tutar Jam'iyyar Brotherhood REUTERS/Amr Abdallah Dalsh

Magoya bayan Jam’iyyar Brotherhood ta ‘Yan uwa musulmi a Masar sun yi wani jerin Gwano na tsawon kilomita daya domin nuna goyon bayansu ga dan takarar Jam’iyyar a zaben shugaban kasa.

Talla

Masu jerin Gwanon sun ratsa birnin Alkahira inda suke rike da rubuce-rubuce da ke nuna goyon bayansu ga Mohammed Mursi wanda wasu masu kididdiga ke ganin ba wani gabansa.

Mursi ya kasance wanda hankalin magya bayan Jam’iyyar ya karkata akan shi bayan Hukumar zaben kasar taki amincewa da mukaddashin Shugaban kungiyar Khairat El-Shata saboda wani zargi da kotun soja ke masa.

Sai dai kuma kungiyar da ke da rinjaye a majalisun kasa ta nuna tana goyon bayanta ga Mohd Mursi wanda tsohon Injiniya ne, kuma ya kasance ba fitacce ba ne, kamar dan takaran na farko da aka dakatar wato Khairat El-Shater.

Bisa irin kididdigan da wasu masana a kasar suka yi na nuna cewa Amr Musa tsohon Ministan waje na kasar, da kuma tsohon Fira Minista Ahmed Shafiq na kan gaba a zaben da za’a yi.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.