Sharhin Jaridu

Sharhin wasu Jaridun Afrika 18 Mayu 2012

Jaridu a Taswirar Africa
Jaridu a Taswirar Africa

Sharhin Jaridun ya mayar da hankali ga Jaridun Najeriya inda danbarwan siyasa ta kunno kai bayan Gwamnonin Arewa 19 sun goyi bayan kalaman Janar Muhammadu Buhari wanda ya yi gargadin barkewar rikici idan aka samu magudin zabe a 2015.

Talla

Jaridar Daily Trust ta wallafa dalla-dalla, kalaman Tsohon shugaban a lokacn da yake karbar bakuncin tawagar Jam’iyyar CPC daga Jahar Niger a Kaduna.

A ranar Alhamis Gwamnonin Arewa sun fitar da wata sanarwa inda suka ce kalaman Buhari gaskiya ne, a wani mataki na mayar da martani ga wasu da suka dauki kalaman tsohon shugaban da wata manufa.

“Baraka ga shugaba Goodluck Jonathan: Gwamnonin Arewa sun kare Buhari” shi ne babban labarin jaridar The Punch.

“Jonathan zai sa a kama ni” inji Buhari a wani labari da aka buga a jaridar Sun a wata jita-jita daga wata hira da Jaridar Premium Times ta yi da Buba Galadima Sakataren Jam’iyyar CPC.

Jaridar The Nation ta buga labari akan martanin da Fadar shugaban kasa da Jam’iyyar PDP mai mulki, inda suka danganta Janar Muhammadu Buhari a matsayin jagoran neman tashin hankali wanda ya fadi zabe a jere da jere.

A nata bangaren Jaridar The Nigerian Tribune ta buga labarin wata kungiyar ‘Yan siyasa a Lagos ta League for Political Parties wadanda suka nemi Buhari ya janye kalaman shi.

Amma Jaridar Guardian da This Day sun ce Jam’iyyar adawa ta ACN ta goyi bayan kalaman Janar Muhammadu Buhari tare da sukar martanin da Jam’iyyar PDP ta mayar game da kalaman tsohon shugaban.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.