ECOWAS-Guinea Bissau

Tawagar Farko ta Dakarun ECOWAS sun isa Guinea Bissau

Dakarun ECOWAS daga Burkina Faso, tawagar farko da suka fara isa kasar Guinea Bissau
Dakarun ECOWAS daga Burkina Faso, tawagar farko da suka fara isa kasar Guinea Bissau AFP PHOTO /ALFA BA

Tawagar farko ta dakarun Kasashen Yammacin Afrika sun isa kasar Guinea-Bissau daga Burkina Faso, a wani yunkurin dawo da zaman lafiya a kasar, bayan Sojoji sun hambarar da gwamnatin farar hula a watan jiya.

Talla

‘Yan sanda da sojojin kasar ta Guinea Bisau, tare da wakilan Majalisar Dinkin Duniya da na kungiyar ECOWAS ne suka tarbi sojan na kasar Burkina Faso.

Jim kadan kafin isar sojan, ECOWAS, ta bayar da sanarwar tura tawagar mai sojoji fiye da 600, don karbar aiki daga hannun sojan kasar Angola, da kuma bayar da goyon baya don dawo da mulkin farar hula.

Najeriya dai na daya daga cikin kasashen da suka ce zasu bayar da gudunmuwar dakaru zuwa Guinea Bissau.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.