Angola

kungiyoyi masu zaman kansu na zargin gwamnati kasar Angola da yin kane kane a harakokin shara'ar kasar

Suzana Inglês, Presidente da Comissão Nacional Eleitoral de Angola
Suzana Inglês, Presidente da Comissão Nacional Eleitoral de Angola http://www.cne.ao/presidente.cfm

Wata kungiya mai zaman kanta a kasar Angola dake fafatukar neman shara’a, Zaman Lafiya da kuma democradiya, a yau litanin ta zargi gwamnatin kasar da yin kane kane a cikin harakokin shara’ar kasarbayan matakin da kotun kolin kasar ta dauka na amincewa da nada wata ta kusa ga gwamnatin kasar a matsayin shugabar hukumar zabe.Shugaban kungiyar ta AJPD Antonio Ventura ya bayyana bakin cikinsu kan amincewa da kotun kolin ta yi da uwargida Ingles, a kan mukamin shugaban hukumar zaben, wanda yace matakin ya fito ne daga gwamnatin kasar, da ta kanainaye komai, a daidai lokacin da ake shirin gudanar da babban zabe a kasar.